Wq/ha/William Shakespeare
Suna da kofofin fita da na shiga; sannan kuma mutum daya a lokacinsa yakan taka rawa a bangarori da dama…
~ Jaques a cikin Kamar Yadda Kake So
![](https://cdn.statically.io/img/upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/06/Julius_Caesar_Coustou_Louvre_MR1798.jpg/220px-Julius_Caesar_Coustou_Louvre_MR1798.jpg)
William Shakespeare (26 April 1564 (baptiza) – 23 April 1616), ya kasance mawaki ne dan kasa Ingila, marubucin wasanni kuma dan wasan kwaikwaiyo, wanda ake dauka a matsayin marubucin harshen Turanci da yafi kowa fice, kuma dan wasan dirama da yafi kowa a duniya.
Maganganu[edit | edit source]
![](https://cdn.statically.io/img/upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/f/fb/Cobbe_portrait_of_Shakespeare.jpg/220px-Cobbe_portrait_of_Shakespeare.jpg)
Ta fito da karya fili, sannan ta kawo gaskiya zuwa haske.
![](https://cdn.statically.io/img/upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/2/24/Shakespeare_grave_-Stratford-upon-Avon_-3June2007.jpg/220px-Shakespeare_grave_-Stratford-upon-Avon_-3June2007.jpg)
Sannan tsinuwa sun tabbata ga wanda ya matsar da ƙasusuwa na.
- Duk abinda ba za’a iya watsi da shi ba dole a rungume shi.
- Kyawu da kanshi kan jawo hankali
Na idanun maza ba sai da mai jawabi ba.- The Rape of Lucrece (1594).
- Nasarar zamani shine ya natsar da sarakuna masu jayayya,
Ya fito da karya fili, sannan ya kawo gaskiya zuwa haske.- The Rape of Lucrece.
- Yarinta da tsufa bazasu taba rayuwa tare ba
Yarinta na cike da nishadi, tsufa na cike da kula wa.- The Passionate Pilgrim: A Madrigal; akwai dan kokwanto game da wanda ya kirkiro wannan.
Romeo and Juliet (1595)[edit | edit source]
- Menene acikin suna? Wanda muke kira da rose,
daga nan duk wani suna zai yi dadi.- Juliet, Act II, scene ii.